المقيت
كلمة (المُقيت) في اللغة اسم فاعل من الفعل (أقاتَ) ومضارعه...
Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah".
Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masõya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfãni ba kuma haka bã su tũre wata cũta?" Ka ce: "Shin makãho da mai gani sunã daidaita? Kõ shin duhu da haske sunã daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abõkan tãrayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da jũna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kõme kuma Shĩ ne Maɗaukaki, Marinjãyi."